Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar tokwaransa na kasar Saudiya da kuma kum ashugaban hukumar lamuni ta duniya, wato IMF.
Abdulnaser Himmati ya bayyana cewa manufae taron itaa ce tattauna hanyoyin bukasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa . Har’ila yau taron tana son kyuatata dangantakar tattalin arziki a kasashen yankin Asia da kuma aiki tare da sauran kasashen duniya sabota ci gaban kasashen duniya gaba daya.
Taron na kwanaki biyu, wata dam ace ga kasar Iran ta bunkasa dangantakarta da sauran kasashen duniya.