Ministan Makamashi Na Iran Ya Yaba Da Yin Aiki Tare Da Kungiyar “Brics”

Ministan makamashi na Iran   ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci taron kungiyar Bricks a kasar Rasha domin halartar taron da aka yin

Ministan makamashi na Iran   ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci taron kungiyar Bricks a kasar Rasha domin halartar taron da aka yin a minstoci akan makamashi.

Bugu da kari ministan ya ce, Tehran yana da sha’awar bunkasa alakarta ta makamashi da Moscow, da kuma sauran kasashen mambobi na kungiyar.

Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya bayar da labarin cewa; Ministan makamashin Abbas Ali Abadi zai gabatar da shawarwari dangane da yadda za a bunkasa hanyoyin aiki tare a tsakanin kasashe mambobi na kungiyar musamman a fagagen masana’antu da kuma fasaha.

Abbas Ali Abadi ya yi ishara da muhimmancin wannan taron bisa la’akari da cewa, wasu daga cikin mambobinsa suna cikin manyan kasashen da suke samar da makamashi, yayin da wasu kuma suke a matsayin masu saye.

A bayan fagen taron,an yi ganawa a tsakanin ministan makamashin na Iran Abbas Ali Abadi da takwaransa na Rasha da kuma wasu manyan jami’an kasar Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments