Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu.
A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin shekaru 10 da suka gabata, tare da bayyana wa takwaransa na kasar Switzerland sabbin ci gaba da suka shafi tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.