Ministan Harkokin Waken Falasdinu Ta Yi Kira Ga Karin Kasashe Su Amince Da Samuwar Kasarta

Ministan harkokin wajen Falasdinawa Varsen Aghabekian Shahin, ta godewa kasashen  duniya da suka amince da samuwar kasar Falasdinu ya zuwa yanzu kuma kuma wadanda suke

Ministan harkokin wajen Falasdinawa Varsen Aghabekian Shahin, ta godewa kasashen  duniya da suka amince da samuwar kasar Falasdinu ya zuwa yanzu kuma kuma wadanda suke shirin yinhaka, sannan tana kodaitar da sauran kasashen duniya da su yi hakan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shahin tana fadar haka a taron yan jarida da ta kira a yau Lahadi a birnin Ramallah, sannan ta kara da cewa ya zuwa yanzu kasashe da dama  sun bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu, Kuma sakone mai kyau ga Falasdinwa, kuma banda haka wannan sakonnin fata ne na samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta.

Ta kara da cewa, amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta yana nufin HKI bata da iko a kanta.

Daga karshe ta bayyana cewa mamayar da HKI takewa kasar Falasdini shi sharrin da ya shafi dukkan yankin. A cikin yan kwanakin nan ne ake saran kasashen duniya da dama zasu bayyana amincewarsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta a taron babban zauren MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted