Ministan Harkokin Wajen Kasar Pakistan Ya Jaddada Bukatar Kyautata Dankon Zumunci Da JMI

Ministan harkokin wajen kasar Pakistan ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa a shirye take ta kyautata danganta da kasashe kawayen Pakistan daga ciki har da JMI.

Ministan harkokin wajen kasar Pakistan ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa a shirye take ta kyautata danganta da kasashe kawayen Pakistan daga ciki har da JMI.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani taro dangane shirin kasar na kyautata dangantaka da kasashen makwabta wadanda suka gada da kasashen yankin Tekun farisa da kuma sauran kasshen Asia.

Mohammad Ishak Dor ya kara da cewa, kasar Pakistan tana da iyaka da JMI wanda ya kai kilomita 900. Don haka tana daga cikin kasashe wadanda suka fi kusa da ita.

Ishak Dor wanda kuma shi ne mataimakin firai ministan kasar ta Pakistan ya kammala da cewa kasar Pakistan tana da kekyawar dangantaka da kasar Iran tun bayan samun yenci a shekara 1947.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments