Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa bayanan baya bayan nan da hukumar kula d makamashin nukiliya ta duniya  da ministan harkokin

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa bayanan baya bayan nan da hukumar kula d makamashin nukiliya ta duniya  da ministan harkokin wajen Oman suka fitar na cewa iran bata kokarin kera makamin nukiliya ya karyata ikirarin da Amurka da HKI ke yi kan shirin nata.

Babban darakata janar na hukumar IAEA a baya bayan nan ya fayyace cewa iran bata kokarin kera makamin nukiliya da kuma kasar Oman babbar mai shiga tsakanin da aka amincewa tsakanin iran da Amurka, yace wadannan kalamai zasu iya bude kofar sake koma teburin tattaunawa tsakanin Iran da kuma kasashen duniya.

Rafeal Grossi ya fitar da sanarwar cewa iran bata neman kera makamin nukiliya shi ma ministan harkokin wajen oman Al-busaidi ya kara tabbatar da cewa babu wata barazanar kera makamin nukiliya a iran, Aracshi ya zargi isra’ila da Amurka da yada parfaganda mara tushe domin wanke ayyukan su na ta’addanci, kuma ya bukacesu da su kama hanyar diplomasiya.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments