Search
Close this search box.

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Takwaransa Na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Rahotanni sun bayyana cewa minsitan harkokin waje na Hadaddiyar  daular larabawa Abdullah bn zayid alinahyan ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran

Rahotanni sun bayyana cewa minsitan harkokin waje na Hadaddiyar  daular larabawa Abdullah bn zayid alinahyan ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran Amir Abdallahiyan game da irin ci gaban da ake ciki a yankin Gaza na irin ci gaba da tafka laifuffuka da israila ke yi kan alummar falasdinu,da kuma muhimmancin kawo karshen taddancin Isra’ila a gaza da gaggauta aikewa da taimakon agaji ,

Haka zalika bangarorin biyu sun bukaci a kafa wani kwamitin hadin guiwa na tattalin arziki domin duba hanyoyin da za’a bi wajen kara bunkasa alakar dake tsakani .

A zantawar ta su ministan harkokin wajen na iran ya nuna damuwarsa na afkuwar ambaliyar ruwa mai tsanani a hadaddiyar daular larabawa kuma ya bayyan shirin iran na taimakawa alummar kasar da wannan bala’I ya shafa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments