A Amurka daruruwan jami’an yan sanda ne suka mamaye jami’ar Columbia da ke birnin New York, inda suka tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa.
rahotanni sun nuna yadda yan sandan sukayi amfani da kwaranga wajen dirar wa dalibai a cikin makarantar, inda har ma suka yi awon gaba da wasu daga cikin masu zanga-zangar.
Tun da farko dai, jami’ar ta gargadi daliban makarantar kan su dakatar da zanga-zangar ko su fuskanci hukuncin kora.
Ko baya ga hakan wasu rahotannin sun ce : an samu hatsaniya a jami’ar California tsakanin masu zanga-zangar nuna goyon baya da kuma masu kin jinin Falasdinawa.
Lamarin ya faru ne lokacin da gungun masu zanga-zangar goyon bayan Isra’ila suka rika yin jifa da turakun da aka sanya domin killace masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa.
A halin da ake ciki dai Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa na ci gaba da yaduwa a jami’o’in Amurka.
Ko a Jami’ar Los Angeles ma an yi irin wannan zanga zanga a wannan Laraba.
Sama da mutum 1000 ne aka kama cikin mako biyu sanadiyyar zanga-zangar, a cewar rahotannin.