Malaysia Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Tashi Wajen Ganin An Yi Wa Falasdinu Adalci

Kasar Malaysia, ta bukaci kasashen Larabawa da na Musulmi da su tashi haikan domin ganin an yi wa Falasdinu Adalci da kuma tabbatar da cewa

Kasar Malaysia, ta bukaci kasashen Larabawa da na Musulmi da su tashi haikan domin ganin an yi wa Falasdinu Adalci da kuma tabbatar da cewa an hukunta Isra’ila Kan Laifikan data aikatawa falasdinawa.

Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim, shi ne ya bayyana hakan inda ya yi kira ga kasashen larabawan da na musulmi da su ci gaba da yin tsayin daka” wajen neman a yi wa Falasdinu adalci da kuma tabbatar da cewa an hukunta Isra’ila kan dukkan laifuffuka da cin zarafin da ta yi wa Falasdinawa tsawon shekaru da dama.

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a gefen taron tattalin arzikin duniya a birnin Riyadh ranar Talata.

M. Anwar ya ce “muna bayyana rashin amincewarsu ga mamayewar da Isra’ila ke wa Falasdinu, wanda shi ne babban abin da ya haifar da wannan rikici da ake ci ciki tsawon lokaci.”

Malaysia dai ta kasance mai goyon bayan Falasdinawa tsawon lokaci.

A cikin watan Disambar 2023, gwamnatin Malaysia ta sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa mallakar wani kamfanin jigilar kayayyaki na Isra’ila daga shiga tashar jiragen ruwanta a matsayin martani ga kisan gilla da Isra’ila ke wa Falasdinawa a zirin Gaza.

A ranar 20 ga watan Disamba ne Malaysiya ta sanar da matakin sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa ga kamfanin ZIM, na jigilar kayayyaki mafi girma a Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments