Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Ya Tattauna Da Ministocin Harkokin Wajen  Kungiyar Da 8

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakhiri Kani ya tattauna da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar D8 daga ciki har da ministocin harkokin wajen

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakhiri Kani ya tattauna da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar D8 daga ciki har da ministocin harkokin wajen kasashen Indonasiya da Pakisatn.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Bakhiri Kani ya gana da ministan harkokin wajen kasar Indonasia Retno Marsudi a gefen taron kasashenn kungiyar D8. Ministan ya bukaci kara dankon zaumunci da kasar Indonasia a matsayinta na kasa mai muhimmanci a nahiyar Asia.

Ya kuma bukashi kwamitin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu su gudanar da taro don gano daga inda za’a tashi a cikin al-amuran raya tattalin arzikin kasashen biyu.

Kani ya kara da cewa ta’asan da HKI take aikatawa a Gaza wani al-amari wanda ya zama dole ga dukkan mutane masu hankali musamman musulmi su dauke shi da muhimmanci su kuba bada gudumawarsu ga Falasdinwa wadanda aka zalunta.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Indonasia ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da ta cimma da JMI . Sannan a shirye take ta taimakawa kasar Falasdinu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments