Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi da manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar labanon Jean Arnault sun tattauna kan ci gaban da aka samu a kasar labanon da yanki da tsaro da kuma batun yarjejeniyar dakatar da yaki da aka kulla takanin iran da Amurka.
wakilin na majalisar dinkin duniya ya mika taaziyyar shahadar jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah sayyid Ali khamina’I da sauran wanda suka yi shahada sakamakon hare-haren da Amurka da isra’ila suka kai kan kasar iran, kuma yadda jaddada game da muhimmancin daukar matakin dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin yankin baki daya.
haka zalika yayi wa ministan takaitaccen bayani game da ci gaba da aka samu a baya bayannan a kasar labanon da kuma kokarin da majalisar dinkin duniya ke yi na ganin an yi aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma taimakawa wajen ganin an kawo karshen rikicin.
Anasa bangaren ministan harkokin wajen iran Abass Araqchi ya godewa manzon musamman na majalisar dinkin duniya kuma yayi tir da ci gaba da kai haramtaccen hari da Amurka ke yi kan iran, da kuma yin fatali da dukkan yarjejeniyar da aka cimma game da mashigar Hurmuz da kuma ci gba da kai harin soji da hki ke yi a kudancin labanon