Ministan Harkokin Wajen kasar Iran Ya Ce Tsaron Tekun Farisa, Na Kasashen Yankin Ne Kawai

Ministan harkokin wajen kasar kasar Iran ya bayyana cewa tsaron tekun farisa yana hannun kasashen yankin ne kawai. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran

Ministan harkokin wajen kasar kasar Iran ya bayyana cewa tsaron tekun farisa yana hannun kasashen yankin ne kawai.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Amir Hussain Abdullahiyan yana fadar haka ne a wani sakon da ya aikewa taron na raya ‘Ranar Tekun Farisa’ a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa kasashen da suke bakin ruwan tekun farisa ne kawai zasu iya samar da tsaro a tekun.

Sannan saboda muhimmancin tekun a yankin Asiya ta kudu da Asiya ta yamma, yakamata kasashen da abin ya shafi su dauki nauyin kula da tsaronsa. Abdullahiyan ya ce jiragen ruwan da suke fitowa daga tekun suna zirga zirgan da kayaki na kasashen yankin zuwa tekunan Medeterinia, Maliya da Atlantika da Pacific. Ministan ya kamala da cewa sunan ‘Tekun Farisa’ da aka bawa ruwan yankin ya dade kuma haka yake a cikin abubuwan da hukumar UNESCO take dauke a matsayin abin tarihi ga kasashen duniya.

A ranar 10 ga watan Urdi Behesht na ko wace shekara, wanda yayi dai dai da 29 ga watan Afrilu, shi ne ranar da turawan Potigal wadanda suke mamaye da tekun farisa har zuwa shekara ta 1622 suke fice daga kudancin kasar Iran. Don haka ne aka sanya ranar a matsayin ranar tekun farisa a kasar iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments