Ministan Harkokin Wajen Iran Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar, inda Ya Gana Da Shugaban Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Alkahira

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi a yau Litinin.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya isa birnin Alkahira da yammacin jiya Lahadi domin tattaunawa da manyan jami’an kasar Masar.

A yayin wannan ziyara, Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi inda suka tattauna batutuwan baya-bayan nan a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da ci gaban yankin, musamman batun kalubalantar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu batutuwan kasa da kasa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da Shirin ministan harkokin wajen Iran na ziyartar ministan harkokin wajen kasar Masar da Lebanon a wani taron manema labarai da ya kira a yammacin ranar Asabar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments