Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi gargadin illar da ke tattare da ci gaba da yaduwar tashe-tashen hankulan ‘yan sahayoniyya a yankin
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyed Abbas Araqchi ya yi gargadin sakamakon karuwar laifukan da yahudawan sahayoniyya ke aikatawa a Zirin Gaza da Gabar Yammacin kogin Jordan.
Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a yau Litinin cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya tana neman ta hanyar ci gaba da laifukan da take aikatawa a Gaza ta kuma nausa bakar aniyarta zuwa gudanar da kashe-kashe jama’a a gabar yammacin kogin Jordan, don tada hankula a yankin Gabas ta Tsakiya tare da mayar da shi zuwa wani rikici mai hatsari.
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya kara da cewa: Idan masu goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na yammacin Turai suka yi watsi da kawo karshen dagewar da yahudawan sahayoniyya suke yi wajen habaka ayyukansu na tada zaune tsaye da aikata laifuka, to suna tarayyar da su a laifukan kuma suna da alhakin daukar duk wata ta’asa na wadannan muggan ayyuka.