Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya soki kungiyar Tarayyar Turai kan gazawarta wajen daukar matakin dakatar da yakin kisan kiyashin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Gaza da kuma mummunan yakin da take yi kan kasar Labanon.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwararsa ta kasar Finland Elina Valtonen a wannan Laraba, Araghchi ya koka kan yadda wasu kasashen Turai suka dauki matakin siyasa mai harshen damo wadda take cin karo da juna dangane da laifukan Isra’ila.
Ministan na Iran ya ce tushen rikicin da ke faruwa a yankin ya ta’allaka ne a fagen yaki da kisan kiyashi da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke yi.
Valtonen ta bayyana damuwarta game da matsaloli da ake fuskanta wajen gudanar da ayyukan jin kai a yankin. Ta ce: “Ina fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali za su dawo a yankin nan bad a jimawa ba.”
Ta jaddada cewa dakatar da tashin hankali na bukatar tattaunawa da tuntubar dukkan bangarorin da abin ya shafa.
Ministocin biyu sun jaddada wajabcin yin shawarwari da nufin fadada huldar dake tsakanin kasashen biyu da karfafa hadin gwiwar ofisoshin jakadancinsu a fagage na diflomasiyya.