Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka kai harin.
A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da ministar harkokin wajen Sweden Maria Malmer Stenergård, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma na ofishin jakadancin.
A yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin kasar Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka aikata wannan lamari tare da daukar matakan da suka dace don hana sake aukuwar lamarin.
Araghchi ya kuma bayyana dangantakar dake tsakanin Tehran da Stockholm tare da jaddada bukatar yin zurfafa tuntuba domin warware rashin fahimtar juna da inganta hadin gwiwar kasashen biyu.
A nata bangaren, ministar harkokin wajen kasar Sweden ta jaddada aniyar kasarta na kare cibiyoyin diflomasiyyar Iran, tana mai jaddada cewa Stockholm za ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.