Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin.
Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Araqchi ya jaddada muhimmancin daukar matakin hadin gwiwa da kasashen yankin domin gaggauta dakatar da laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, da kuma tsagaita bude wuta a zirin Gaza, lamarin da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen warware wasu rikice-rikice a yankin yammacin Asiya.
Jami’an biyu sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, sakamakon ci gaba da kai hare-hare da mamayar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, Lebanon da Syria, da kuma ci gaba da kai hare-hare ta sama da Amurka ke yi kan kasar Yemen.
Araqchi da Abdelatty sun jaddada wajabcin inganta yunƙurin diflomasiyya don kawar da tashe-tashen hankula da hana barkewar rikici a duk faɗin yankin.
Har ila yau, sun tattauna kan tattaunawar da aka shirya yi tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka, wadda za a yi a wannan Asabar mai zuwa a birnin Muscat na kasar Oman.