Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Soki Rahoton Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Kan Kasarsa

Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen kasar

Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya soki sabon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran yayin ganawarsa da babban darektan hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya Rafa’el Grossi a birnin Alkahira.

A yayin taron, wanda aka gudanar a babban birnin Masar bisa bukatar Grossi, Araqchi ya tunatar da hukumar ta IAEA da babban daraktan ta game da alhakin da ya rataya a wuyansu na gudanar da ayyukansu cikin kwarewa.

Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya soki zarge-zarge marasa tushe da ke kunshe cikin sabon rahoton hukumar ta IAEA kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya tare da jaddada cewa bai kamata hukumar ta IAEA ta amince mai tasirantuwa da matsin lamba na siyasa da kuma manufar wasu kasashe mambobin kungiyar ba.

Bayan ganawar, Grossi ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi, wanda yake ziyara a birnin Alkahira, a gaban ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments