Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa; Yahudawan Sahayoniyya Sun Kasa Murkushe Gwagwarmaya

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su.

Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata.

Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar  gwagwarmayar da al’ummar Falastinu suke yi na neman ‘yancin kai daga ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya tsawon shekaru 80 da suka gabata, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya taya al’ummar Falasdinu murnar samun nasara mai dimbin tarihi da suka samu da kuma juriya kan kisan kiyashin da suka fuskanta daga yahudawan sahyoniya a Gaza na tsawon watanni goma sha shida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments