Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Isa Iraki Domin Tattauna Halin Da Ake Ciki A Syria

 A yau Juma’a ne minstan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, Abbas Arakci ya isa birnin Bagadaza domin halartar taron da zai hada kasashe uku;

 A yau Juma’a ne minstan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, Abbas Arakci ya isa birnin Bagadaza domin halartar taron da zai hada kasashe uku; Iran, Iraki, Syria.

Shi ma minstan harkokin Syria tuni yana birnin Bagadaza kamar yadda kamfanin dillancin labarun “Isna” ya ambata.

 Manufar taron na kasashe uku dai shi ne tattauna halin da ake ciki a kasar Syria wacce take fuskantar munanan hare-hare daga ‘yan ta’adda dake samun goyon bayan Isra’ila da kuma Amurka.

Dama dai a ranar Lahadin da ta gabata ministan harkokin harkokin wajen na Iran ya ziyarci birnin  Damascus inda ya tattauna halin da ake ciki  a Syria. Daga Syria ne ya wuce ya zuwa kasar Turkiya inda ya tattauna da jami’an gwamnatin kasar akan kai da komowar ‘yan ta’adda da suke kama manyan biranen Arewacin kasar ta Syria.

A cikin kasa da mako daya ‘kungiyar “Tahrirus-sham” wacce asalinta alka’ida ce, ta kame garuruwan Idlib, Halab da kuma Hama.

Sojojin Syria sun ce sun fice daga birnin Hama ne domin sake jan daga bisa dacewa da yanayin da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments