Ministan harkokin wajen Iran yayi kashedi ga kasashen Turai cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wani matakin kare hakkinta
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi kasashen Turai kan daukar duk wani mummunan mataki kan Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, yana mai jaddada cewa; Iran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani keta hakkinta.
Abbas Araqchi ya rubuta a ranar Juma’a a cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin X cewa: “Maimakon yin aiki da kyakkyawar niyya, Tawagar Turai ta zaɓi ɗaukar munanan matakai kan Iran a kwamitin alkalan hukumar IAEA.” Ya kara da cewa: “Lokacin da wadannan kasashe uku suka rungumi dabi’ar kuskure iri daya a shekara ta 2005, sakamako ne na sabbin al’amura suka fito a fuskoki da dama, ciki har da kai Iran ga gagarumin matsayin inganta sinadarin Uranium a cikin kasarta. Shin har yanzu tawagar kasashen Turai ba su koyi wani darasi ba cikin shekaru ashirin da suka gabata a mu’amalarsu da Iran?” Ya ci gaba da cewa: Zarge-zargen da ake yi kan Iran da tuhumarta da karya yarjejeniyar tsaro – bisa ga rahotanni masu rarrafe da siyasa – a fili yana nufin haifar da neman rikici ne. Turai na gab da sake fuskantar wani babban kuskuren dabarun.