Search
Close this search box.

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Iran Ta Amince Da Duk Shawarar Da Al’ummar Falasdinu Ta Yanke

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada goyon bayan Iran ga duk wata yarjejeniya da al’ummar Falasdinu da ‘yan gwagwarmaya suka amince da ita Khalil

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada goyon bayan Iran ga duk wata yarjejeniya da al’ummar Falasdinu da ‘yan gwagwarmaya suka amince da ita

Khalil Al-Hayya mamba na ofishin siyasa kuma mai kula da huldar Larabawa da Musulunci a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ya taya Abbas Araqchi murnar zabensa da aka yi a matsayin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A yayin ganawar jami’an biyu ta hanyar wayar tarho, Al-Hayya ya tabo batun halin da ake ciki kan tattaunawar tsagaita bude wuta a Zirin Gaza, da laifukan baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a yankunan da suka mamaye, da kuma kokarin da wannan gwamnati ‘yar mamaya take yi na neman sauya halin da Masallacin Al-Aqsa ke ciki.

Al-Hayya ya yaba da irin kokarin da tsohon ministan harkokin wajen Iran shahidi Amir Abdullahian yake yi wajen nuna goyon baya ga ‘yan gwagwarmaya da al’ummar Falastinu, ya kuma jaddada cewa: Al’ummar Falastinu suna yabon yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran take ci gaba da goyon bayan manufofin Falastinawa da kuma gwagwarmayarsu na kalubalantar muggan laifukan ‘yan sahayoniyya.

A nasa bangaren, Abbas Araqchi ya mika godiyarsa ga Malam Khalil Al-Hayya bisa wannan kira da taya shi murna da ya yi, sannan ya jaddada cewa matakin da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran take dauka na tallafa wa al’ummar Falastinu da ake zalunta a gwamnati ta goma sha hudu za ta ci gaba da karfi.

Araqchi ya kuma jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta goyi bayan duk wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin Gaza wanda al’ummar Falastinu ‘yar gwagwarmaya da sauran kungiyoyin gwagwarmaya da kuma kungiyar Hamas suka amince da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments