Ofishin Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike bayan kisan gillar da sojojin Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a ranar Alhamis a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, bayan sun daga hannayensu suka mika wuya.
“Mun firgita da kisan gillar da ‘yan sandan kan iyaka na Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a Jenin, a Yammacin Kogin Jordan ” in ji mai magana da yawun Babban Kwamishinan Jeremy Laurence ga manema labarai.
“Babban Kwamishinan (Volker Türk) ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaggawa, kuma ya bukaci a hukunta wadanda suka aikata wadannan laifukan,”
Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna mutane biyu suna fitowa daga wani gini da sojojin Isra’ila suka kewaye, suna daga hannayensu, Sannan aka gan su kwance a kasa a gaban sojojin kafin a mayar da su cikin ginin, inda Sojojin Isra’ila suka bude wuta, suka kashe mutanen biyu.
Hukumar Falasdinawa ta yi Allah wadai da Isra’ila kuma ta bayyana kisan a matsayin kisan gillar da aka yi a fili.
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa ta bayyana mutanen biyu da aka kashe a matsayin Muntasir Qassem Abdullah, mai shekaru 26, da Youssef Assa’sa, mai shekaru 37, inda ta ce sojojin mamayar Isra’ila na tsare gawarwakinsu.