Kwararru na MDD sun bada rahoton cewa tsakanin sojojin 3000-4000 na kasar Ruwanda ne suke aiki kafada da kafada da mayakan kungiyar yan tawaye ta M23 na gabacin kasar Kongo wadanda suke samun manya-manyan nasarori a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa’ News’ ya bayyana cewa a ranar Laraban da ta gabata ce wadannan kwararru suka fidda rahoto kan hakan, mai shafuka 293. Ya kuma kara da cewa, goyon bayan da gwamnatin kasar Ruwanda take bawa yan tawaye na M23 ya sabawa dokokin kasa da kasa, sannan yana iya zama laifin da yakamata a dorawa kasar Rwanda takunkuman tattalin arziki.
Yankin gabacin kongo dai ya dade yana fama da yan tawaye, wadanda yawansu ya kai 120, ko wace kungiya akwai abinda ya sa ta dauki makamai. Amma duk da haka kuma suna neman iko da yankin Kivu, ko saboda kabilanci ko don kare kansu.
AFP yace shugaban kasar Kongo Felix tsetsekedi, Amurka da kuma MDD duk suna zargin kasar Ruwanda da taimakawa yan tawayen na M23. Labarin ya kara da cewa sojojin kasar Ruwanda suna tarwatse a yankunan gabacin kongo kuma sun fito ne daga runduna ta 2th da ta 4TH na sojojin kasar Ruwanda. Kamar yadda wata majiya kusa da kungiyin M23 ta fada masa.