Ministan Harkokin Wajen Siriya Ya Ziyarci Kasar Qatar A Dai Dai Lokacinda Kasar Take Bukatar Amincewar Kasashen Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Siriya ya gana da tokwaransa na kasar Qatar da kuma Firai ministan kasar a kokarin da kasar take yi na samun

Ministan harkokin wajen kasar Siriya ya gana da tokwaransa na kasar Qatar da kuma Firai ministan kasar a kokarin da kasar take yi na samun amincewar kasashen duniya da kuma kasashen yankin.

Shugaban kasar ta Siriya Ahmed Jolani ya bayyana cewa kasarsa tana neman Amincewa daga kasashen duniya musamman kasashen yamma da kasashen yankin. Kungiyar yan ta’addar ta Hai’at tarirar Asham, ta kwace iko da kasar  Siriya a ranar 8 ga watan Decemba bayan da tsohon shugaban kasar Bashar Al-Asad ya fice da ga kasar, tare da taimakon sojojin kasar Rasa.

Kafin haka dai Al-Shibani ya gana da ministan harkokin wajen kasar Saudiya da wasu Jami’an gwamnatin kasar ta Saudiya. Sannan a ranar jumma’an da ta gabata ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da kuma Faransa a birnin Damascus babban birnin kasar.

Daga shekara ta 2011 ya zuwa faduwar gwamnatin Asad an kashe mutane kasar Siriya kimani 500,000 tsakanin sojojin kasar da magoya bayansu da kuma yan tawaye.

Al-Shaibani ya bayyana cewa fiye da kashi 90 na mutanen kasar Siriya suna rayuwa cikin talauci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments