MDD : Isra’ila Ta Ki Amincewa Da Kashi 85% Na Rabon Kayan Agaji A Gaza

Kwamitin Sulhu na MDD ya gana cikin gaggawa a ranar Laraba, bisa bukatar Aljeriya, domin tattauna tabarbarewar al’amuran jin kai ga ‘yan  Gaza da suka

Kwamitin Sulhu na MDD ya gana cikin gaggawa a ranar Laraba, bisa bukatar Aljeriya, domin tattauna tabarbarewar al’amuran jin kai ga ‘yan  Gaza da suka rasa matsugunansu a arewacin yankin, tun farkon rikicin.

MDD ta bayyana cewa Isra’ila ta ki amincewa da kashi 85% na rabon kayan agaji a arewacin Gaza tsawon makonni biyu.

A game da hakan dai Gwamnatin Washington ta yi barazanar dakatar da wani bangare na taimakon da take bai wa Isra’ila idan lamarin bai daidaitu ba.

A cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (Ocha), mutane 55,000 ne suka bar yankin Jabaliya sakamakon tsananin fadan.

Mutane kuma 400,000 da suka makale a kewayen Jabaliya sun fara rasa ruwa da abinci.

Babu motocin agaji da suka tsallaka cikin yankin Falasdinawa tsakanin ranakun 2 zuwa 15 ga watan Oktoba duk da wannan mawuyacin hali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments