Mayakan Hizbullah Sun Halaka Sojojin Yahudawa Tare Da Jikkata Wasu Na Daban

Sojojin yahudawan sahayoniyya 5 ne suka halaka kuma wasu 15 suka jikkata a wani gumurzu da suka yi da mayakan kungiyar Hizbullah a kan iyakar

Sojojin yahudawan sahayoniyya 5 ne suka halaka kuma wasu 15 suka jikkata a wani gumurzu da suka yi da mayakan kungiyar Hizbullah a kan iyakar kasar Lebanon

Kafofin yada labaran ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya sun bayyana faruwar wani sabon matakin tsaro mai wahala da sojojin yahudawan sahayoniyya suka fuskanta a yakin da suke yi da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullah a kan iyakar Lebanon da Falasdinu.

Kafafen yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun ruwaito cewa: Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Lebanon ya yi sanadin halakan sojojin Isra’ila 5 tare da raunata wasu 15.

Shafin yanar gizo na “Hadshot Bazaman” na yahudawan sahayoniyya sun sanar da cewa: An hango jiragen sama masu saukar ungulu na sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suna sauka domin kwasar sojojin da suka jikkata don kai su asibitin Rambam da ke Haifa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments