Rahotanni sun bayyana cewa matatar man fetur din Dan Gote ta sanar da sabon farshin litar mai gidajen mai da dauran dilolin mai a fadin kasar akan N699 a duk lita daya, kuma yayi kira ga masu gidajen mai da su yi rijista domin samun wannan garabasa
Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Alhamis a hukumance daga matatar mai din ta dan gote inda ya gayyaci dukkan gidajen mai da dilolin mai masu zaman kansu a fadin kasar da su shigo cikin sabon tsarin nata.
Haka zalika kamfanin mai din yace nan gaba kasan zaa sanar da karin tallafin kayayyakin ga sabon shirin,inda za ta fara jigilar daukar mai din kyauta har zuwa gidan mai.
kamfanin yayi amanna cewa kaddamar da sabon shirin zai yi tasiri sosai a farashin mai a fadin kasar da kuma daidaito wajen samar da kayayyakin, musamman ganin yadda Dillalan mai din ke ci gaba da daidaita wa da kasuwar mai da aka soke a nigeriya