Masu jerin gwano sun gudanar da gangami a gaban ofishin MDD dake nan Tehran inda suka bukaci Majalisar ta kori HKI, musamman bayan da kotun ICC ta fidda sammacin kama firai ministan HKI Da Kuma tsohon ministansa na yaki Gallants.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa masu jerin gwanon sun allawadai da manya manyan kasashen duniya wadanda suke goyon bayan HKI a kissan kiyashin da take yi a Gaza tun fiye da shekara guda. Sannan sun allawadai da Amurka a matsayin ta na kasa babba wacce take tallafawa yahudawan na sahyoniyya.
A jiya Alhamis ce kotun ICC mai hukunta masu manya manyan laifuffuka a karon farko ta fidda sammacin kama wani shugaba daga cikin shugabannin da suke tare da kasashen yamma a cikin shekari 22 da kafata.
Kotun tana zargin Firai ministan HKI Benyamin Natanyaghu da tsohon ministansa na yaki da take hakkin bil-adama da kuma laifufukan yaki a gaza daga ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa 24 ga watan Mayun shekra ta 2024 a bisa shaidun da suka shiga hannunta.
Wannan hukuncin dai ya rikita shuwagababbin mafi yawan kasashen yamma, saboda yadda suke da hannu dumu dumu a taimkawa HKI a cikin ta’asan da take aikatawa a Gaza fiye da shekara guda.
Masu jerin gwanon sun bukaci duk wadanda suke fada a ji a duniya su kaucewa HKI saboda kissan kiyashin da take yi a gaza da Lebanon.