Masu Goyon Bayan Kasashen Falasdinu Da Lebanon Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Kasashen Montreal Da Canada

Magoya bayan Falasdinwa da kuma kasar Lebanon kasashen a Montreal Da Canada sun gudanar da gagarumar zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga mutanen kasar Falasdinu

Magoya bayan Falasdinwa da kuma kasar Lebanon kasashen a Montreal Da Canada sun gudanar da gagarumar zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga mutanen kasar Falasdinu da kuma Lebanon wadanda sojojin HKI sukewa kissan  gilla tun fiye da shekara guda da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa masu zanga-zangar sun bukaci a kawo karshen kissan kiyashin da akewa Falasdinawa a gaza da kuma mutanen kasar Lebanon. Sun kuma bukaci a kama Firam Ministan HKI Benyamin Natanyaho a gurfanar da shi a gaban kotu don alifufukan take hakkin bil’adama da kuma laifukan yaki da ya aikata.

Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suna dauke da tutocin kasar Lebanon da kuma Falasdinu, sannan suna allawadai da HKI. Labarin ya kammala da cewa  akwai malaman yahudawa da dama da suka halarci zanga zangar suna kuma allawadai da HKI, suna fadar cewa ba da sunansu ne take kissan Falasdinawa a Gaza da kuma kasar Lebanon ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments