Masana Sun Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Zata Rai Na Kanta Idan Ta Yi Gigin Sake Kai Hari Kan Iran

Haramtacciyar kasar Isra’ila zata fuskanci martani mai gauni matukar ta yi kuskuren sake kai hari kan kasar Iran Manazarta da masana harkokin yada labarai na

Haramtacciyar kasar Isra’ila zata fuskanci martani mai gauni matukar ta yi kuskuren sake kai hari kan kasar Iran

Manazarta da masana harkokin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun mayar da hankali ne kan batutuwan matakan wuce gona iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take kai wa kan duk wani bangaren da take ganinsa a matsayin barazana gare ta, inda Farfesa Nabih Awada, ya tabo barazanar da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi wa Iran, da irin hatsarin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata wurga kanta ciki.

Awada ya bayyana cewa: Ana samun sabanin siyasa game da wajibcin kaddamar da harin soji kan Iran, yayin da ake tattaunawa kan yadda sojoji ke iya haifar da babbar hasara ga haramtacciyar kasar ta Isra’ila tare da rusa nasarorin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ikirarin cimmawa a Gaza da Lebanon, da kuma ci gaban da take samu kan abin da ke faruwa a Siriya.

Awada ya kara da cewa: Akwai tattaunawa mai tsanani a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma fargabar fuskantar mayar da martani mai girma na Iran dangane da duk wani yunkurin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila zata yi na kai hari kan Iran, yana mai cewa a bisa tsammanin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, idan har ta kai harin soji kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, hakan na iya haifar da wani gagarumin harin mayar da martani kanta, baya ga halin tsaka mai wuya da ta shiga dangane da hare-haren da take fuskanta daga ‘yan gwagwarmayar Yemen musamman yadda makamai masu linzamin Yemen ke ratsa duk wurin da ake son tarwatsawa a haramtacciyar  kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments