Manyan Cibiyoyin Kudi Na Duniya Sun Yi Gargadai Akan Sabbin Kudaden Fito Na Amurka

Kungiyar kasuwanci ta duniya  ( WTO) da asusun bayar da lamuni           ( IMF) sun yi gargadi akan sakamakon dake tattare da Karin kudaden fito na

Kungiyar kasuwanci ta duniya  ( WTO) da asusun bayar da lamuni           ( IMF) sun yi gargadi akan sakamakon dake tattare da Karin kudaden fito na kasuwanci da gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump ta yi a jiya Alhamis.

 Kungiyar kasuwancin ta duniya, ta yi hasashen cewa ci gaban harkokin kasuwanci a duniya zai sami koma baya da kaso 1% a cikin 2025, wanda hakan yake nufin akasin yadda aka yi hasashe tun da fari.

Babbar daraktar kungiyar kasuwancin ta duniya Ngoz Okonjo-Iweala ta yi gargadin cewa, Karin kudaden fito da aka yi zai iya jefa duniya cikin yakin kasuwanci,  idan kuwa kasashe su ka dauki matakin mayar da martani, to za a sami tsaiko a cikin harkokin kasuwanci a duniya.

Shi kuwa asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ta bakin shugabarsa Kristalina Ivanova Georgieva, ya bayyana cewa; Wadannan matakan da aka dauka za  jawo hatsari mai girma wajen ci gaban da tattalin arzikin duniya yake yi, musamman ma a wannan lokacin da dama ake fama da tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin na duniya yake yi.

A gobe Asabar ne dai sabon harajin na Amurka zai fara aiki, wanda ya fara daga Karin 10% akan kayan da ake shigar da su Amurka, zuwa fiye da haka gwargwadon yadda ake da gibi a tsakanin kowace kasa da Amurkan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments