Har yanzu Moscow ba ta ga wani mataki na gaske da zai kawo karshen zubar da jini a yankin Gabas ta Tsakiya ba, in ji ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov a karshen ziyararsa a Malaysia.
Lavrov ya ce “Babu wani mataki wanda aka dauka da zai kawo karshen wannan zubar da jini har yanzu. Isra’ila tab akin firaminista Benjamin Netanyahu, ta sha mai da martani ga kiran tsagaita bude wuta cikin gaggawa da cewa ba za ta tsaya ba har sai ta ruguza Hamas gaba daya.”
Ya bayyana cewa, “A ganina, – kuma da yawa daga cikin takwarorina suna da wannan ra’ayi – aiki ne da ba zai yiwu ba a ruguza wata kungiya da ke da ita gaba daya, kuma tana da gagarumin goyon baya a ciki har da kasashen musulmi.”
Babban jami’in diflomasiyyar na Rasha ya kara da cewa, wasu kasashe na kokarin tsara sabbin shawarwarin sasantawa da nufin kawo karshen tashin hankalin, “idan Isra’ila ta ki amincewa da tsagaita bude wuta nan take.”
Ya ce wasu kasashen Larabawa, Masar da Qatar suna aiki tare da Amurkawa, kuma suna gudanar da wasu tarurruka da Isra’ilawa.
Sai dai ministan harkokin wajen Rasha ya nunar da cewa “ba shi da kyau a ce an cire Falasdinawa daga tarurrukan da aka tsara domin sanin makomarsu.”