Manjo Janar Salami Ya Ce; Kungiyoyin Gwagwarmaya A Duk Inda Suke Suna Cin Gashin Kansu Ne

Manjo Janar Salami ya bayyana cewa: Duk wani lungu da sako da ‘yan gwagwarmaya suke suna aiki ne don kare kasarsu kuma bisa manufofinsu Babban

Manjo Janar Salami ya bayyana cewa: Duk wani lungu da sako da ‘yan gwagwarmaya suke suna aiki ne don kare kasarsu kuma bisa manufofinsu

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husain Salami ya jaddada cewa: Kowane bangare na gwagwarmayar yana aiki ne a kasarsa kuma daidai da manufofinsa, sannan ya ce: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna kare Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce da dukkanin kasarsu, kuma zukatansu natse da kyakkyawan fatansu, da kuma tsayayyen matakan da suka dauka na zama tushen karfi ga al’ummarsu madaukakiya a fadin kasar.

Manjo Janar Salami ya taya murna a yayin kammala taron addu’o’in kasa karo na biyu da dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka dauki nauyin gudanarwa, wanda aka gudanar a cikin jirgin ruwan “Shahidi Rudaki” a garin Bandar Abbas, dangane da zagayowar ranar haihuwar shugabara matan talikai Sayyidah Fatima Al-Zahra (a. s), yana cewa: “Ya yi farin cikin kasancewa a yau a cikin tsakiyar Tekun Fasha, cikin masu kare iyakokin Allah. Wadannan jarumai masu kwarewa da suke kare kimar kasa da ‘yancinta da kuma daukakarta daga makiya, ta hanyar sadaukar da rayukansu da dukkan abin da suka mallaka zukatansu cike da nutsuwa da babban fata mai girma a kan tsayayyun matakai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments