Bama-bamai na Mark 84 da Amurka ta kera ba su buƙatar karin haske, lallai sun kasance abin da ya fi daukar hankalin duniya a lokacin kazamin yakin da aka yi a zirin Gaza, saboda barnar da suka yi da kuma kashe-kashen jama’a da ba a taba gani ba.
Wadannan bama-bamai su ne suka fi yaduwa a fagen yakin Gaza, kuma sun fi barna da halaka a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare kan al’ummar Gaza. Tunawa da su yana da alaƙa da mummunan kisan kiyashi da al’amuran zubar da jini da suka girgiza duniya.
Daga cikin wadannan bala’o’i har da kisan kiyashin da aka yi a asibitin Baptist, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa kusan 500. Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Guzurin Amurka ce ga Yahudawan Sahayoniyya, kamar yadda kafar yada labarai ta yahudawa ta biyu ta watsa, baya ga rahoton da jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta buga, cewa wanda ya kai hari kan Asibitin Baptist da wannan makami ba matukin jirgin Isra’ila ba ne, a’a ma’aikacin Amurka ne a rundunar sojin saman Amurka, wanda ya yi amfani da bam mai lamba Mark 84 daga cikin jirginsa wajen kai harin. Wannan ya bayyana irin yadda Amurka ke da hannu kai tsaye wajen kai hare-hare a yankin zirin Gaza.