Makaman Yemen Sun Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Abha Da Ke Kasar Saudiya

Sojojin kasar Yemen sun cilla makamai masu linzami da makaman Drones kan tashar jiragen sama na Abha da ke yammacin kasar ta saudiya, bayan luguden

Sojojin kasar Yemen sun cilla makamai masu linzami da makaman Drones kan tashar jiragen sama na Abha da ke yammacin kasar ta saudiya, bayan luguden wuta wanda jiragen yakin kasar Saudia suka yi kan tashar jiragen sama ta Sana’a a jiya don hana kayakin agaji isa birnin San’a daga Tehran.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Litinin ce Jirgin fasinja daga kamafanin Mahan na kasar Iran ta tashi daga birnin Tehran zuwa San’a babban birnin kasar Yemen , dau da wasu yemenawa da kuma kayakin agaji don kawo karshen killacewra da saudia da Amurka suka yiwa kasar na kimani shekaru 10 da suka gabata.

Jefa boma boman da Saudia ta yi kan tashar jiragen sama na San’a ya hana jirgin Mahan sauka a birnin San’a amma maimakon haka ta sau a birnin Hudaida nab akin tekun Malia tare da kayakin agajin da kuma yemenawa.

Iran ta yi allawadai da hana jirgin agajin sauka a birnin San’a, ta kuma kara da cewa yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

A wani bangaren kuma gwamnatin Ansarullah wadanda suke iko da yemen sun gargidi kasar Saudiya kan bude sabon yaki tsakanin kasashen biyu, sannan ta yi barazanar tana iya rufe mashigar ruwa ta babul mandab, wanda mai yuwa ya daga farashin mai a duniya zuwa dalar Amurka $200 a kan ko wani ganga.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted