Makamai masu linzami na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun fada kana birnin na uku a HKI wato Haifa a safiyar yau Jumma’a, inda ta tsallaka dukkan garkuawan makamai masi linzami na HKI ta je ta sami bararta ba tare da kuskure ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto tashar talabijin ta ” Channel 12″ tana tabbatar da cewa makamai masu linzami daga kasar Lebanon sun fada kan birnin. Kuma an ji tashin jiniyar gargadi a birnin Haifa da kewajensa.
Kafin haka dai jiragen yakin HKI sun kai hare hare a kan kudancin kasar Lebanon inda suka kasha mutane akalla 9 daga ciki har da wata mata mai ciki.
Har’ila yau majiyar kungiyar Hizbullah ta bada snaarwan cewa ta cilla makamai masu linzami samfurin Fadi-1 kan garin Kiryat Ata wanda ke kan iyaka da birnin Haifa na kasar Falasdinu da aka mamaye.
Kungiyar ta ci gaba da maida martani babu kakkautawa kan hare haren da jiragen yakin HKI suke kaiwa kan kasar ta Lebanon kwamani 5 da suka gabata.
Ya zuwa yanzu hare haren HKI kan kasar Lebanon ya kai ga shahadar mutane 700 da kuma raunata wasu, 2000.