Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da takwaransa na Saudiyya kan batutuwan da suka shafi kasashensu da kuma batun Falasdinu
Mukaddashin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ali Baqiri ya tattauna da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ta hanyar wayar tarho, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashensu da kuma halin da ake ciki a Falasdinu gami da hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suke kai wa kan al’ummar Falasdinu.
A cikin wannan tattaunawar a yammacin jiya Juma’a, Baqiri ya yi godiya kan ire-iren taimakon da gwamnatin Saudiyya ta yi ga mahajjata musamman alhazan Iran.
Kamar yadda Baqiri ya tabo batun halartar mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin kan kasashen Asiya karo na goma sha tara da aka gudanar a birnin Tehran, inda ya yi nuni kan irin ci gaban da aka samu da hadin gwiwa tsakanin Iran da Saudiyya tare da bayyana shi a matsayin abin alfahari.
Baqiri ya kuma yi ishara da ci gaba da aikata munanan laifukan yaki da yahudawan sahayoniyya suke yi kan al’ummar Falastinu a Zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan, da kuma jaddada barazanar da yahudawan sahayoniyya suke yi kan kasar Labanon a matsayin wani ci gaba da aikata laifuka kan bil’Adama. Yana mai fayyace cewa: Manufofin yahudawan sahayoniyya suna matsayin manyan barazana ga dukkan yankin Gabas ta Tsakiya.