Sojojin Amurka,HKI Da Larabawa Sun Gudanar Da Taron Sirri

Majiyar sojojin kasar Iran ta bada sanarwan awkuwar taro a asirce na manya-manyan kwamandojin sojojin Amurka, HKI, da wasu kasashen Larabawa a asirce a kasar

Majiyar sojojin kasar Iran ta bada sanarwan awkuwar taro a asirce na manya-manyan kwamandojin sojojin Amurka, HKI, da wasu kasashen Larabawa a asirce a kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labarun Tasnim na kasar Iran, ya nakalto cibiyar khatamul Anbiya tana fadar cewa ta sami labarin ne a ranar 20 ga watan satumban da muke ciki, kan cewa gwamnatin Amurka ta yanke shawarar sake farwa kasar Iran da yaki. Don haka aka gudanar da wannan taron a wani wuri a kasar Jamus, don aiwatar da wannan shirin.

Labarin ya kara da cewa, mai yuwa an gudanar da taron tun kafin 15 ga watan Satumba, amma bai bayyana ba sai a rananr.

Kuma kasashen da abin ya shafa sun hada da Kwamandan CENTCOM na Amurka, Saudia, UAE, HKI, Bahrain, Kuwaita, Qatar, Jordan da Masar. Kuma babu wata kasa da aka ambata wacce ta musanta halattar taron ko tabbatarwa. Har’ila yau sun tattaun batun tallafawa Sudia kan kasar Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted