Majiyar Fadar Shugaban Kasar Amurka Tace Ta Shiga Tattaunawa Kai Tsaye Da Kungiyar Hamas A Gaza

Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza

Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza kai tsaye.

Tashar talabijin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto Karoline Leavitt tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya aiki Adam Boehler mutumin da yake wakiltansa a al-amuran fursinonin Amurka a waje, zuwa kasashen yankin kudancin Asiya don tattauna batun Amurkawa da suke hannun kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

Leavitt ta kara da cewa Amurkawa sun cancanci a shiga tattaunawa ko kuma a bi duk hanyoyin da suka dace don ganin, an kubutar da Amurka wadanda suka shiga hanun makiyansu a ko ina suke a duniya.

Wannan labarin yana zuwa ne a lokacinda fadar ta white hause ta bayyana kungiyar Hamas a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Hamas ta fara kama Amurkawa ta tsare tun shekara 1997 bayan da Amurka ta fito fili tana goyon bayan HKI kan kisan kiyashin da takewa Falasdinawa a Gaza da sauran wurare.

Rahoton ya kara da cewa Amurka ta fara tattaunawa da kungiyar ne a birnin Doha na kasar Qatar a cikin yan makonnin da suka gabata.

A halin yanzu dai Hamas tana rike da fursinoni 59 daga cikin 240 da suka kama a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments