Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa
Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15.
Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai.
A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda 18 suka nuna adawarsu da kudurin, yayin da wakilai 14 suka ki kada kuri’a.