Babban maga takardar majsaliar dinkin duniya Antonio Gutteres yayi gargadi game da halin da ake ciki a yammacin Asiya cewa kuskure daya tak idan aka yi zai iya jefa duniya cikin mummunan bala’I da baa taba ganin irinsa ba,
Hazalika ya nuna damuwarsa matuka game da halin da yankin yamamcin Asiya ke ciki sakamakon laifukan da Isra’ila ke tafkawa yace yankin yan gab da fadawa cikin wani mawuyacin hali da ba zai yi wa kowa dadi ba idan ba’a kai zuciya nesa ba
Ya ce kara rikicewa yanayi a yankin yana bukatar goyon bayan kokarin da ake yi cikin kyakkyawar niyya na ganin a lalubo hanyar samar da sulhu a yammacin Asiya da kuma kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, domin itace hanyar mafi dacewa ta kawokarshen tashin tashina dake faruwa a yankin.