Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza

Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza.

A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba amma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri.

Ta bayyana cewa kin bari a shigar da kayayyakin jin kai na yankunan Falasdinawa tun daga ranar 2 ga watan Maris ya kara ta’azzara wahalhalun jin kai a Gaza, tana mai bayanin cewa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na kokarin samar da muhimman abubuwan da ake bukata domin ci gaba da rayuwar al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments