Rahotannin da suke fitowa daga kasar Saudiya sun bayyana cewa mahajjata daga kasashen duniya daban dabn kimani 1100 ne suka rasa rayukansui saboda tsananin zafi a kasar ta Saudiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto rahoton na cewa wannan shi ne zafin mafi muni da aka yi tun shekara ta 2015.
Rahoton ya kara da cewa a zuwa ranar Alhamis da ta gabata daga cikin mutane 658 da suka mutu sanadiyyar zafin daga kasar Masar ne, kuma ba’a yi rijistar 630 daga cikinsu.
Gwamnatin saudiya ta kara da cewa da alamun mafi yawan wadanda suka mutu basu da damar samun na’uran sanyay dade ko inda suke.
Ya kuma kara da cewa kasashe 10 ne suka bada rahoton mutuwar mahajjata 1,081 yan kasashensu. Aikin hajji dai daya ne daga cikin ginshikan aiki hajji, wajibi ne ga duk musulmin da yake da ikon zuwa ya je.
Daga nan kasar Iran dai hukumar mahajjatan kasar ta bada sanarwan mutuwar mutane 11 ya zuwa yanzu sanadiyyar tsananin zafin.
Kasar Pakistan wacce mahajjata 150,000 suka je kasar saudia don aikin Hajjin bana ta bayyana cewa mutane 58 ne suka mutu. Indonasia 183, bai kai mutane 313 da suka mutu a bara.
Hari la yau kasashen India, Jordan, Iran, Senegal, Tunisia, Sudan da Iraq suka bada sanarwan mutuwar mutanen kasashensu.