Mafi Yawan Mutanen Gaza Sun Rasa Muhallansu Sakamakon Hare-Haren Isra’ila

A cewar jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, Falasdinawa miliyan 1.9, wato  kashi 80% na al’ummar yankin, sun rasa

A cewar jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, Falasdinawa miliyan 1.9, wato  kashi 80% na al’ummar yankin, sun rasa matsugunansu, yana mai nuna matukar damuwa game da umarnin ficewa daga Khan Younis da Isra’ila tat a baiwa mazauna birnin.

Da safiyar yau, Isra’ila taumurci Falasdinawa da aka tilasta yin  gudun hijira da karfi zuwa birni na biyu mafi girma a zirin Gaza, wato Khan Younis, da wadanda ke zaune a wurin, da su sake “kaura”, yayin da hare-haren sojojin mamaya na Isra’ila ke ci gaba da kara tsananta, lamarin ad ke nuni da cewa babu wani wuri mai aminci a cikin yankin zirin Gaza.

An kuma bayar da rahoton cewa, Falasdinawa a Khan Younis sun samu sakonnin murya daga lambobin wayar da Isra’ila ta yi musu na umarce su da su bar gidajensu. Zeinab Abu Jazar da ta yi gudun hijira zuwa Khan Younis a farkon yakin, ta ce “Mun sami sako ta wayar hannu”  kan mu gagaguta yin kaura.

Sigrid Kaag jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya yayi jawabi ga kwamitin sulhu yana gargadin cewa “Sama da mutane miliyan 1.9 yanzu suna gudun hijira a fadin Gaza … Ina cikin  matukar damuwa dangane da rahotannin da ke cewa Isra’ila ta umarci Falastinawa das u fice daga wasu yankunan na Khan Yunis.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments