Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean

A taron CELAC da Tarayyar Turai karo na biyar a Colombia, shugabannin Latin Amurka sun yi Allah wadai da karuwar jibge sojojin Amurka a yankin

A taron CELAC da Tarayyar Turai karo na biyar a Colombia, shugabannin Latin Amurka sun yi Allah wadai da karuwar jibge  sojojin Amurka a yankin Caribbean, suna gargadi game da tsoma bakin kasashen waje da kuma yin kira da a hada karfi da karfe wajen kare ‘yancin kai da zaman lafiya.

Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya aika wa kasashe mambobin CELAC wasika yana mai kira da su yi tir da abin da ya bayyana a matsayin tsokana da neman tyar da zaune tsaye da Amurka ke yi a yankin Caribbean.

Da yake magana kan hare-haren da aka kai kwanan nan kan jiragen ruwa na kamun kifi da kuma tura sojojin Amurka kusa da iyakokin ruwa na Venezuela, Maduro ya bayyana cewa akwai bukatar a hada karfi da karfe a matsayin kasashe kuma a cikin murya daya domin dakatar da hare-hare da barazanar soja ga mutanen yankin.

Maduro ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan gillar da aka yi ba bisa ka’ida ba a teku, wanda a baya aka yi Allah wadai da shi.

Wasikar ta jaddada bukatar samar da hanyoyin hadin gwiwa na jin kai don kare ‘yancin yankin Latin, da kuma kin mika wuya ga masu son yi babakere a kan arzikin da Allah ya huwace wa al’ummomin yankin, da kuma hana su cimma wannan manufa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted