Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza.
A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa su “tsaurara matsayinsu na hadin gwiwa” kan Isra’ila, “idan babu wani mataki da ya dace da yanayin jin kai, a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa” a zirin Gaza.
Macron ya ce, “Katange ayyukan jin kai yana haifar da yanayi mara kyau,” yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Singapore Lawrence Wong.
Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ta kakaba wa Gaza takunkumin hana agajin jin kai na tsawon watanni kusan uku.
Isra’ila dai ta zargi Macron da kasancewa a cikin “yan tawaye” ga gwamnatin tel-Aviv bayan da shugaban Faransa ya ce dole ne kasashen Turai su tsaurara matakansu na hadin gwiwa kan Isra’ila idan har ba a dauki matakin jin kai ba.
Gwamnatin Isra’ila dai ta yi kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi dangane da bala’in karancin abinci a Gaza, tana mai cewa ya ba da izinin kai kayan agajin a karkashin wani sabon tsarin hadin guiwa da Amurka.