Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa: Mutane 3,754 ne suka yi shahada, yayin da wasu 15,626 suka samu raunuka tun bayan fara kai farmakin sojojin Isra’ila kan kasar
Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan kasar Lebanon ya karu.
Ma’aikatar ta kara da cewa: A cikin wani takaitaccen bayani da ta fitar ta ce: Hare-haren wuce gona da iri kan kasar Lebanon, ya yi sanadin shahidan mutane 3,754, yayin da wasu 15,626 suka jikkata, tun bayan fara kai farmakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi kan kasar.
Ma’aikatar ta ce adadin ya karu ne bayan da wasu mutane 29 suka yi shahada tare da jikkatan wasu 67 na daban a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.