Ma’aikatar Lafiya A Gaza: Adadin Wadanda Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila Ya Kai 38,584

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce akalla mutane 38,584 ne suka mutu a yakin da Isra’ila ta yi kan yankin da aka yi wa kawanya.

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce akalla mutane 38,584 ne suka mutu a yakin da Isra’ila ta yi kan yankin da aka yi wa kawanya.

Adadin wadanda suka mutun ya ƙunshi mutuwar mutum 141 a cikin sa’o’i 24, in ji sanarwar ma’aikatar, ta kuma kara da cewa mutum 88,881 ne suka jikkata a Gaza tun bayan fara yakin.

Jami’an bayar da agaji na farar hula a Gaza sun zaƙulo gawawwaki 21 na Falasɗinawa daga cikin ɓarguzai a ranar Lahadi bayan wani hari da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.

Wata majiya daga bangaren kiwon lafiya ta bayyana cewa an gano gawar mutum shida sakamakon harin da Isra’ila ta kai a birnin Rafah inda aka kai su asibitin Khan Younis.

Haka kuma an ƙara zaƙulo wasu gawawwakin uku daga cikin ɓaraguzai a yammacin Gaza, kamar yadda Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta bayyana a wata sanarwa.

Jami’an sun ƙara gano wasu gawawwakin goma a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin Gaza.

Sai kuma mazauna sansanin gudun hijira na Nuseirat sun gano gawawwakin mutum biyu a tsakiyar Zirin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments