Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: HKI Ta Wuce Haddi A Tsokanar Kasar

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa gwamnatin HKI ta wuce gona da iri a tsokanan kasar Iran, saboda kissan

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa gwamnatin HKI ta wuce gona da iri a tsokanan kasar Iran, saboda kissan shugaban kungiyar Hamas a cikin kasar da tayi, sannan tace daukar fansar jininsa ya zama wajibi gareta.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Kani yana fadar haka a zantawarsa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Pakistan kuma mataimakin firai ministan kasar Muhammad Ishaq-Dor a jiya Asabar.

Bakiri ya kara da cewa shahid Isma’ila Haniya shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas wacce take fafatawa da HKI a gaza kimani watanni 10 da suka gabata, bako ne a kasar Iran ya kuma kara da cewa kasheshi a kasar Iran keta babbar jan layi na JMI ne.

A ranar Laraba 31 ga watan Yulin da ya gabata ne, wasu ma’aikatan HKI a nan Tehran suka cilla makami mai nauyin kilogram 7 daga wani wuri kusa da masaukin Haniyya a nan Tehran, inda fashewar makamin yayi sanadiyyar shahadarsa da kuma wanda yake tsaronsa.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Pakistan kuma mataimakin Firai ministan kasar Muhammad Ishaq-dor ya yi allawadai da kissan Haniyya sannan ya bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan al-ummar Falasdinu sannan tana goyon bayan a gudanar da taron gaggawa na kasashen musulmi don sanin matakan da yakamata a dauka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments